Tarihi

Ina Kogon Masu Barci Bakwai yake (Ashabul Kahfi ) كهف الرقيم ?



Amman, Jordan.

Akwai wani kogo kusa da Birnin Amman na kasar Jordan, wanda kuma aka fi sani da kogon masu barci bakwai, wanda ke da wasu ƙananan kaburbura takwas da aka rufe a ciki da kuma wani bututun samun iska da ke fitowa daga cikin kogon.

Al-Kahf, ko Kogon Masu Barci Bakwai, Yana Kan hanya ne daga Amman zuwa ga Tekun Gishiri.

Wurin da ke kauyen Rajib da ke da tazarar kilomita 10 daga gabas Da Amman Babban Birni Kasar Jordan, Yana bude kowace rana da karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma kuma kyauta ne Shiga.

Har yanzu akwai sauran muhawara game da ainihin inda wannan kogon yake, wasu Suna cewa yana cikin kasar Turkiyya in da suka hada da Afşin, Tarsus, da Mount Pion.

Ganowa da Haƙa ƙasa

A cikin Shekarar 1951, Wani ɗan jaridar Jordan Taysir Thabyan ya gano Kogon Ashabul Kahfi, Har ya buga hotunan Kogon a mujallar sojojin Siriya, tare da sanar da Sashen Kula da Tarihi na Jordan. Sashen ya sanya wani masanin binciken kayan tarihi na Jordan din Rafiq al-Dajani aikin bincike a cikin kogon. Sun sami ƙananan kaburbura takwas a cikin babban kogon, tare da ƙasusuwan mutane.

A Cikin Alkur’ani Mai Girma

Alkur’ani Mai Girma ya labarto mana tarihin magabata irin su ashabul Kahfi ba don mutanen ba ne, sai dai don mu fa’idantu da halin da suka shiga sannan kuma suka tsare imaninsu.

Wannan Qissa ta Ashabul Kahfi Kur’ani ya hakaito ta ne a lokacin da Mushi*rikan Quraishawa su ke son Jaraba Annabi SAW, sai suka tambayi Yahudawa cewa wacce irin jarabawa za su yima Annabi SAW. Akan hakane Yahudawa suka fadamu cewa su tambaye shi akan wasu mutane da suka shiga cikin kogo, da wani mutumin da ya zagaye duniya, da Ruhi (RAI).

Suratul Kahfi tana dauke da bayanin Ashabul Kahfi, wato wasu matasa su bakwai (7) tare da karensu, da suka rayu a zamanin mulkin wani azzalumin sarki Daqayanusa bayan Annabi Isa AS ko kafin zuwansa da sheraka 250. A zamanin ana bautan gumakane karkashin wannan sarki, a garin Amman da ke kasar Jordan a yau.

Sai matasan su 7 suka kyamaci bautan wannin Allah, kuma suka yi imani da Allah sannan suka yi hijira don tsoron tsananin azabar da sarkin zai yi musu idan yakamasu.

Matasan sun gudune don su tsira da Imaninsu, kuma suka shiga wani kogon dutse. Bayan shigarsu sai Allah yasa musu barci tsawon shekaru 300 ko 309 a kirgar watan sama. Sannan Allah ya tashe su daga barcin cikin hikimar sa.

Alkur’ani mai Girma ya ambata wannan kissa kuma a da sauran littafan kiristanci da na tarihi. Amma akwai sabani da yawa a cikin tarihin wadannan bayin Allah, Kamar haka:

1. Adadin su.

2. Kasar da kogon da suka boye.

3. Shin kafin zuwan Annabi Isa ne ko bayan zuwan sa ne.

4. Sunayen su, da sauran wasu bayanai da yawa.

Allahu A’lamu

See also  Cikakken Tarihin Taliya (Spaghetti)

.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button