Addu'o'i
Addu’a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi
Addu’a Ga Mara Lafiya Idan Aka Ziyarce Shi:
Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance idan ya ziyarci mara lafiya sai yace masa;
لاَ بَأْسَ طَهُورٌ إِنْ شَاءَ اللهُ .
La ba’asa tahoorun in sha’al-lah.
Ba komai, tsarkaka ce in Allah ya yarda.
أَسْأَلُ اللهَ الْعَظِيمُ، رَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ أَنْ يَشْفِيكَ .(سبع مرات)
Asalul-lahal-‘azeem rabbal-‘arshil-‘azeem an yashfeek (7).
Ina rokon Allah mai girma, Ubangijin Al’arshi mai girma, ya warkar da kai. (sau bakwa).
Manzon Allah, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya ce; “Babu wani bawa Musulmi da zai ziyarci mara lafiya wanda ajalinsa bai riga ya zo ba, sannan ya fadi wannan (addu’a) sau bakwai face ya sami lafiya”.