BusinessLife StyleTech

Menene Amazon KDP, da kuma yadda ake samun kuɗi dashi a internet?

Amazon KDP maɓuɓɓugar samun kuɗi online ga ɗalibai..

Kuna baccin ku daloli sunata zaɓaɓɓaka acikin account ɗinku ta hanyar Amazon KDP cikin sauƙi batare da wani ilimi mai zurfi ba kawai Abunda ake buƙata shine sanin menene Amazon KDP?

Amazon KDP na nufin babbbar kasuwar sayar da litattafai a duniya
Wato Kindle Direct Publishing.
Ba Dole bane ku zama ƙwararrun marubuta ba a’a kawai kuna buƙatar samun gaɓa mai muhimmancin gaske domin yin rubutu.

Menene Kindle Direct Publishing(KDP)?

Shine ɓangaren hada-hada da kasuwancin littafi na babbar kasuwar online ta duniya “AMAZON” mallakar wani ɗan kasuwa daga cikin jerin masu arziƙi a duniya ‘JEFF BEZOS’ wacce tafaro a 2007 a yau KDP yana da Shekara 16 a (2023) KDP yana bada damar ɗora littattafai kyauta ba tare da kuɗin talla ba, kuma kuna samun kuɗaɗe masu yawa ta hanyar wannan littafin ta hanyar tallatawa a faɗin duniya, a duk lokacin da wani ya saya ko ya karanta zaku samu tarin kuɗaɗe.

Abunda kuke buƙata kawai shine ƙirƙirar littattafanku, sanya farashin sa kuma ku ɗora shi, a Amazon KDP,

Kamfanin Amazon ne yake kula da cinikayyar littafan dakuma bugawa tare da sadar dashi ga wanda yasiya idan hard copy yake buƙata.

a Amazon KDP Abunda kawai kuke buƙata Shine: buɗe account a Amazon KDP, samar da wani littafi, yin cover design na littafin, ɗora littafin Amazon KDP, rubuta ɗan bayani a takaice dangane da littafin bayan haka bakwa buƙatar yin sharing ko tallata littafin Amazon ce keda alhakin wannan Kuma dazaran ansiya littafin ku Amazon zata cire 30% na kuɗin aikin data muku na jigilar littafin da tallan sa.

See also  YADDA ZAKA IYA SANIN LAST SEEN NA WANI A WHATSAPP KODA YA RUFE LAST SEEN NASHI

Abun tambayar shine wanne irin littafi ake ɗorawa?

Galibi littafan sun haɗa da:

Novels
Summary na wani littafi
Littafin girke-girke
Littafin koyar da wani ilimi
Littafin labarai da tarihi
Littafin Analysis
Kowacce irin idea ko ilimi akayi littafi aka ɗaura a Amazon za’a siya kuma abun mamakin Shine ba’a buƙatar littafin yazama yanada yawa sosai mostly littafan 12 pages ko ƙasa da haka ma, bugu da ƙari littafan summary suna samun kasuwa Sosai misali wani littafi shahararre mutum ya ɗunkule yayi summary ɗinsa yakuma ɗora a Amazon kokuma wani taƙaiceccen bincike akan wani ɓangare na ilimi.
Kai tsaye domin yin rijistar KDP ku shiga wannan Link Ɗin https://kdp.amazon.com/

Ismail Aliyu Ubale
https://t.me/fasaharalbadar
Albadar Global Agency Ltd
18th February 2023

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button