HUKUNCIN RATAYA LAYA DA GURU!!!!
Tambaya
Assalam Alaikum. Malam, menene l hukuncin amfani da LAYA KO GURU a musulunci?
Allah yasa mu dace.
Amsa
Wa’alaikum assalam, To dan’uwa Layu da guru sun kasu kashi biyu:
1. Layun da aka yi su da Sakandami ko Hatimi ko sunayan aljanu ko wani abu na daban wanda ba Qur’ani ba, wannnan malamai sun cimma daidaito game da haramcinsu kamar yadda ya zo a Fataawaa Allajna Adda’imah 2/212 saboda fadin Annabi ﷺ (LAYU da kuma abin da ake daurawa mace don miji ya sota shirka ne) kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: (3883) kuma Albani ya inganta shi, sannan da hadisin da Imamu Ahmad ya rawaito mai lamba ta: (16969), inda Annabi ﷺ yake cewa: (Wanda ya rataya laya to ya yi shirka, shima wannnan hadisin Albani ya inganta shi a Silsila Sahiha.
Hadisan da suka gabata suna nuna haramcin daura Laya saboda Manzon tsira ya kira ta da shirka, shirka kuma tana fitar da mutum daga musulunci.
2. LAYUN da aka yi su daga Alqur’ani ko hadisai ingantattu, wadannan na’u’i malamai sun yi sabani akansu:
A. Sun halatta saboda sun kunshi sunan Allah da kuma karatun alqur’ani wanda sifar Allah ce, wanda ya dogara da su ya dogara ga Allah, wannan ita ce maganar Amru bn Al-ass da Aisha da wasu daga cikin magabata.
B. Ba su halatta ba saboda Ba’a samu Annabi ﷺ ya yi ba, da hakan shari’a ne da an gan shi ya yi ko da sau daya ne a rayuwarshi, sannan rataya layun da suke dauke da Alqur’ani zai jawo a wulakanta su tun da za’a shiga wurare marasa tsarki da su lokacin biyan bukata, kiyaye hakan kuma yana da kamar wuya.
Zance mafi inganci shi ne haramcin amfani da Layun da suke daga Alqur’ani saboda dukkan alkairi yana cikin biyayya ga Manzon Allah ﷺ, sannan shari’ar musulunci ta halatta mana addu’o’i da yawa na neman kariya wadanda suka wadatar da mu daga layu.
Don neman karin bayani duba: Taisirul Azizil Hamid shafi na: (136) da kuma Ma’arijul Kabul 2/510.
Allah ne mafi sani.
4/10/2017
Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.