Tambayoyi a Musulunci
ZAN IYA AURAN WACCE KISHIYAR MAMANA TA SHAYAR ?
Tambaya
Aslm’ alkm.
Ina yiwa malam fatan alkhairi, ina tambaya ne don Allah akan idan matar mahaifina (Yadikkona) ta shayar da wata mata a gidanmu wanda ba ƴarta ba lokacin ma ni ba’a auri mamata ba, toh zan iya auren wannan matar da aka shayar a gidan mu ko ta zama ƴar ƴar uwata.
Allah Ya kara basira da kuma Ikhlasi.
Amsa
Wa alaikumus salam
Bai halatta ka aure ta ba, saboda da nonon mahaifinka aka shayar da ita, don haka ta zama ‘yar’uwarka.
Allah Madaukakin Sarki ya haramta auran ‘yar’uwa ta fuskar shayarwa a aya ta (22) a suratun Nisa’i.
Allah ne mafi sani.
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa
25/01/2023