Tech

Yadda Zaka Cire Waya A Security Ko Pattern Cikin Sauƙi


Domin amfanuwa ba domin cutarwa ba.

Salisu Abdurrazak Saheel

Da yawan mutane suna faɗawa cikin irin wannan matsalar, kasanya “Password” ko “Pattern” amma sai kazo cireta sai kuma kamanta abinda kasanya dole daga karshe ka kaita wurin masu gyara kabasu aƙalla naira 500 sannan su buɗe maka ita kuma a hakan ma kana iya rasa kayan dake cikin wayar, To in sha Allah yau zanyi bayanin wasu hanyoyi guda biyu da zaka iya cire ko wane irin “Pattern ko Password” cikin sauƙi basai ka kai anci kuɗinka ba..

Note: inata samun mutane suna min Complain akan wannan matsalar ta manta Password wanda dole suna buƙatar wannan hanyar domin cirewa, wasu kuma yan’uwan su ne Allah ya ɗauki rayuwarsu kuma ba’asan Password na wayar nasu ba anaso a buɗe, dan haka saboda irin hakan zanyi wannan rubutun ba domin wani mugu ko ɓarawo yayi amfani da hanyar domin cutarwa ba, duk wanda yayi hakan Allah ya isa ban yafe ba!
Sannan akwai hanyoyin kula da wayoyi da nake yawan posting gudun faruwar hakan sai kubi matakan da nake badawa domin kariya.
Allah ya kyauta.

1. Hanya ta farko idan itace; Misali “Pattern” ɗin wayarka ne kasanya kuma sai akazo akayi rashin sa’a kamanta bakasan yadda zaka cireshi ba, gashi kuma akwai “Email” ɗinka akan wayar da abubuwa da yawa kuma bakaso su goge, saboda sunada muhimmanci, To matakin da zakabi shine; zaka cigaba da jaraba sanya “Pattern” ɗin har sai sun rubuto maka “Try Again In 30 Second” kasan daman hakane idan kamanta “Pattern” ɗinka kuma kanata trying to idan kayi trying da yawa zasu nuna maka “Try again in 30 second” wanda ko ka danna zakaga baya nunawa, To kai tsaye; idan ka lura daga ƙasan wurin sanya pattern ɗin zakaga an rubuta; “Forgot Pin” sai ka danna shi, Zata bayyanar maka da wurin da zaka sanya “Email” da “Password” ɗinka..

See also  Yadda Ake yin Hacking Na Facebook account

To kaikuma sai kasanya “Email” ɗinka da yake akan wayar da “Password” naka, ka tabbatar akwai “Gmail” ɗinka a wayar.

Bayan kasanya zakaga “Sign In” a gefe, sai ka danna shi, kana danna shi shikenan zakaga wayarka ta buɗe Ta bayyanar maka da “Unlock Section”
Zata rubuta maka gashinan kazaɓi wani “Pattern” ɗin da kakeso kasanya, zata baka List ɗinsu kamar haka:

“None”
“Slide”
“Face Unlock”
“Voice Unlock”
“Pattern”
“Pin”
“Password”

Sai kazaɓi wanda kakeso kasanya aciki idan ma bazaka sanya ba kawai sai ka danna “None”. Shikenan kagama da wannan matsalar wayarka zata fita daga “Pattern” ɗin kuma babu abinda zai goge acikinta..

2. Hanya ta biyu; wani lokaci zakaga kasiya waya amma kuma baka sanya “Email” ɗinka akanta ba, kokuma wayar abokinka kuma gashi bayanan kuma kanaso kayi amfani da ita gashi tana cikin “Pattern” kanaso kacireta, to ga hanyar da zakabi domin cireta, zakaje ka danna makashin wayar domin ka kashe wayar da farko, bayan ta mutu, zaka danna wurin ƙara Volume da wurin kunnawa a tare (Idan kuma wayar ƙirar kamfanin samson ce, to zaka danna wannan madannin na tsakiyar ta ɗinnan tareda madannin ƙara Volume da kuma wurin kashewa a tare) to zaka dannesu a tare har sai wayar ta kunnu karka saki harsai ta kunnu.

Bayan ta kunnu zata bayyanar maka da wasu rubututtuka kamar haka:


Robot system now
Power off
Apply update from ADB
Apply update from SD card
Apply update from cache
Wipe data/factory reset..☑️✅✔️
Wipe cache partition
Backup user
Restore user data

To zaka dinga danna makunin rage Volume, zaka dinga danna shi har sai kazo daidai layi na “6”. (Koda da yaren china ta rubuto maka to zakadinga dannawa ne harsai kaje layi na “6”)

See also  YADDA ZA KUYI PIN NA POST DINKU A FACEBOOK

Kana zuwa layi na “6” sai ka danna makunnin kunna waya, kana dannashi zai bayyanar maka da wasu rubututtuka kamar haka;

“Confirm wipe of all user data?”
THIS CANNOT BE UNDONE
No
No
No
No
No
No
No
Yes–Delete all user data..✔️✅☑️
No
No
No

Idan kazo daidai na “8” wato wanda aka rubuta “Yes” sai ka danna makunnin waya, Kana danna shi zaifara “Searching” bayan yagama Searching kai tsaye zai sake bayyanar maka da waɗannan rubututtukan da ya bayyanar maka da farko, to kaikuma anan sai kashiga na farkon wanda zakaga an rubuta “Rebot system now” sai ka danna madannin kashe waya, Kana dannawa zakaga wayar ta kunnu ta cire Security ɗin tagama komai, zakaga ta bayyanar maka da “Welcome” da kuma alamun ka zaɓi yare wato “Language”

Daganan shikenan wayarka tadawo normal ta kunnu amma dai komai dake cikinta zai goge ta dawo sabuwa..

Allah yataimaka

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button