Kimiyya da fasahaTech

YADDA ZAKA HANA WAYARKA YIN ƙARA YAYIN GABATAR DA KO WACCE SALLAH A MASALLACI

Wannan yana da matuƙar amfani ga dukkan musulmi, musamman ma a garemu mu maza, dan haka idan ka sani ka daure ka sanar da wani.

A dalilin muyi ibada ne Allah ya haliccemu, ma’ana Allah ya haliccemu ne domin muyi masa ibada wato bauta kenan, kamar yadda Allah madaukakin sarki ya fa’di acikin littafinshi mai tsarki:
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإِنْسَ إِلَّا لِيَعْبُدُونِ
Wama khalaqtu aljinna waal-insa illa liyaAAbudooni.
Kuma Ban halitta aljannu da mutãne ba sai dõmin su bauta Mini.

To acikin dukkanin ibada kuma babu mafi girma kamar sallah, domin haka ne ta zama abun farko da za’a tambayi bawa a kanta cikin kabarinshi, kunga ya wajaba a garemu mu kyautata sallarmu ta ko wacce irin fuska.

Lura da hakan yasa dole muyi taka tsantsan a yayin da muke gabatar da ibadarmu musallamman ma sallah domin gudun kada mu samu mishkila cikinta.

Mafi yawan lokuta wayoyinmu suna yin ƙara cikin masallaci a yayin da muke gabatar da ibada ne ba tare da son ranmu ba kuma ba tare da muna jin da’din hakan ba, hakanne zaisa kaga dukkan wani wanda ya dauki ibada da muhimmanci ranshi yana 6aci idan wayarshi tayi ƙara a masallaci yayin da ake gabatar da ibada, domin idan tayi ƙarar tana jawo hankalinshi a gareta kuma tana jawo hankulan wasu mutanen harma su saurari irin amon dake fitowa daga cikin wayar, wanda kuwa faruwar hakan kuskurene a wajen duk wani mai gabatar da sallah indai ya dauketa ibada mafi girma.

Tabbas da yawa daga cikin mutane mantuwace take jaza masu shiga masallaci da wayarsu ba tare da sun rufe ƙararta ba.

See also  Bayani a kan Fasahohin Sadarwa: 1G zuwa 6G

Domin magance irin wannan matsalar ta ƙarar waya a masallaci yayin gabatar da ibada sai kubi wannan hanyoyin da zan maku bayani:

1- Da farko zaka shiga cikin playstore ‘dinka kayi download na wannan app ‘din : Auto Silence at Prayer’s Time.

2- Bayan ka bu’deshi zai buƙaci ka bashi damar fara aiki a saman wayarka, ma’ana ka yarje mashi yin aiki a wayarka, sai ka danna mashi “Allow”.

3- Daga nan zai kaika wani waje da zai buƙaci ka danna wani ‘dan ma6alli domin kunnashi app ‘din ya zama active a saman wayarka, nanma sai ka danna wajen.

4- Daga nan zai dawo dakai farkon fuskar app ‘din amma zai chanja maka hoton fuskar tare da nuna maka wani rubutu da yake cewa “ka saita lokutan sallah” sai ka danna wajen shima.

5- Matakin ƙarshe nanne zaka shiga cikin sunan ko wace sallah da aka lissafa a wajen harda ta jumma’a, ka saka lokacin farata da lokacin idar da ita, kamar yadda kuke gani cikin hoto na saita nawa, kaima nasan dole zaka san lokutan da kuke gabar da sallah a masallacinku kaima sai ka saita naka haka.

Indai kayi saitin naka kaima kamar haka, to insha Allah daga lokacin da za’a fara sallah har a idar wayarka ba zatayi ko wane irin ƙara ba insha Allah koda kiranka akayi ko ace an tura maka da saƙo ne.

Allah dayin kuskure ƙarami ko babba a yayin gabatar da ibadarmu, Amin.

Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button