ZAN IYA YIWA DAN SHI’A SALLAMA ?
Tambaya:
Assalamu’alaikum warahaamatullahi wabarakatuhu : Malam shin zan iya yiwa dan Shi’a sallama ?
Amsa:
To dan’uwa Allah da manzonsa sun kwadaitar akan sallama saboda kasancewarta tana sanya soyayya a tsakanin mutane, tana kawo hadin kai tana gusar da kewa, wannan yasa Annabi s.aw. ya yi umarni da sallama, saboda tana kaiwa zuwa Aljanna, kamar yadda hadisin Tirmizi mai lamba ta: 599 ya tabbatar da hakan.
Tabbas ‘yan shi’a suna da akidu wadanda suke warware musulunci, Daga ciki akwai zagin sahabban da Allah ya yarda da su, da riya tawayar qur’anin da Allah ya yi alqawarin kiyaye shi, da siffanta Nana A’isha da mazinaciya duk da Allah ya kubutar da ita daga can saman saman bakwai.
Saidai ba duk mutumin da ya riya abubuwan da suka gabata ba za’a kira shi da kafiri , dole sai an tabbatar da cewa ya yi su ne bisa ilimi, Kuma ba shi da wata Shubha wacce ta kasa warwaruwa.
Yana daga cikin ka’idoji a wajan malaman Tauhidi ba duk wanda ya aikata kafirci ake cewa kafiri ba, don haka jahilai a cikin ‘yan shi’a da gama-gari wadanda suka shiga shi’a saboda talauci ko kuma zaton cewa addinin gaskiya ne ba za mu kafirta su ba,kuma ba za mu ki yi musu sallama ba, ko da kuwa suna riya wadancan abubuwa da suka gabata, saboda akwai hadisai da yawa da suke bada uzuri ga wanda ya aikata kafirci bisa kuskure ko jahilci.
Don haka duk musulmin da ka san an shigar da shi SHI’A a bai-bai saboda jahilcinsa kana iya masa sallama.
kyakykyawar mu’amala tana iya sanyawa mutum ya gane gaskiya, kamar yadda hakan ya faru ga mutane da yawa a zamanin annabi S.a.w. da sahabbansa.
Allah nai mafi sani.
Dr. Jamilu Zarewa
17/1/2016