Tambayoyi a Musulunci

NA TSINCI NAIRA ₦500, KO ZAN IYA AMFANI DA ITA BA TARE DA CIGIYA BA?

                       Tambaya:-
Wani bawan Allah ne ya tsinci Naira: ₦500, a wurin kuma bai ga wadanda zai yi wa cikiya ba…  Ya ya kamata yayi da kudin tsintuwar?,  suna ajiye yanzu haka kusan wata daya.

                          Amsa:-
To dan’uwa idan mutum ya yi tsintuwa ya wajaba a gare shi ya yi cigiya har tsawon shekara guda, idan bai samu mai ita ba, daga nan zai iya amfani da ita, amma in mai ita ya zo daga baya zai biya shi, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 5761.

Amma idan abin da ya tsinta dan kadan ne ba shi da yawa, to ya l halatta ya yi amfani da shi ko da bai yi cigiya ba, saboda abin da aka rawaito cewa: Annabi ﷺ ya ga wani dabino akan hanya, sai ya ce: In ban da ına tsoron na sadaka ne da na ci. Muslim ya rawaito a lamba ta: 2527, sai hadişin ya nuna dan karamin abu ba ya bukatar cigiya.

Malamai şun yi sabani wajan iyakance tsintuwar da ba ta bukatar cigiya, wasu sun ce za’a koma al’adar mutane, duk abin da mutane şuke ganinsa ba a bakin komai ba, to in an tsince shi ba ya bukatar cigiya, Ibnu Khudama ya hakaito daga Imamu Malik cewa: bai wajaba mutum ya yi cigiyar abin da bai Kai a yanke hannu saboda shi ba, wato daya bisa hudun dinari, haka nan sayyadina Aliyu ya tsinci dinare daya ya yi amfani da ita ba tare da yayi cigiya ba.

Abin da ya gabata yana nuna cewa: mutukar ba ka samu mai (₦5,00) din da ka tsinta ba a kusa da Kai, ya halatta ka yi amfani da ita ba tare da cigiya ba, tun ba kudi ne mai yawa ba, kuma mai ita ba zai kwallafa rai Akanta ba.

See also  SHAFA FUSKA BAYAN KAMMALA ADDU'A !

Don neman karin bayani duba: Al-mugni 6/351.

Allah ne mafi Sani.

1/11/2015

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button