LawShehu Rahinat Na'Allah

Ɗaurin Wata 6 ne Hukuncin wanda ya canjawa Motar shi Penti

Marubuci: Shehu Rahinat Na’Allah


Babban burin dokokin Nigeria shine su samar da tsaro da kariya ga kowanne Dan kasa ta ɓangaren rayuwar shi ko kuma dukiyar shi, dan haka akayi dokar da ta haramta ka canjawa Motar ka Penti (Kamar tana baƙa ka mayar da ita fara) saboda motoci a Nigeria ana yimasu rajista ne da Kalar pentin su, dan haka ya zama wajibi duk lokacin da zaka canja ma motar ka kala (Penti) dole sai ka sanar da hukumomin da abun ta shafa sun baka Approval domin su canja maka wani license ɗin sannan kuma ka biya kudin canjawar.
Idan har kayi gaban kanka kaje ka canja ba tare da ka sanar masu ba sun baka Approval, to ka aikata laifin da za’a iya daure ka har na tsawon watanni Shida ko ka biya tarar Kuɗi ₦3,000, ko kuma a haɗe maka duka biyun, biyan tara da kuma zama gidan gyaran hali. Sannan kuma wancan license ɗin da kake dashi na farko yayi expire sai ka canja wani.

Duba Sashi na 13, 231, da 232 National Road Traffic Regulations, 2012.

Bissalam

See also  Menene ya halasta ka fada dangane da addinin wani ko aqidar shi, menene kuma ya haramta a hukumance?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button