MAI YA SA SHUGABANNI KE KOKARIN CIRE TALLAFIN MAI?
A rubutuna na jiya na kawo takaitaccen tarihi da dalilin ya saya aka fara kawo tsarin tallafin mai a Nigeria. Yau kuma za mu yi bayani game da dalilan da ya sanya Gwamnatin Nigeria ke bukatar ta cire tallafin mai gaba daya. Kafin haka bari mu sake waiwayar tarihi.
Bukatar cire tallafin man fetur dai ba sabon abu ba ne a Nigeria, domin Shuganni da yawa sun yi yunkurin cire tallafin mai a lokacinsu amma hakan ya gagara. Misali:
1. A June 20, 2003 Olusegun Obasanjo ya yi yunkurin cire 50% na tallafin mai. A lokacin ana sayar da fetur N26, idan an cire 50% na tallafin litar mai za ta koma N40. Wannan yunkuri bai samu karbuwa ga yan Nigeria ba, kasancewar kungiyar Yan Kwadago watau Nigerian Labor Congress (NLC), wadda Adams Oshiomole ya ke jagoranta a lokacin su ka fada yajin aiki tare da zanga-zanga a ranar June 29, 2003. Lokacin an yi dauki ba dadi tsakanin kungiyar Yan Kwadago da shugaban kasa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 sakamakon wutar da jami’an tsaro su ka budewa masu zanga-zangar. Lamarin da ya dauki hankulan shuganni kasashen duniya har wasu daga ciki su ka shiga maganar. Hatta Gwamnoni musamman Bola Ahmed Tunubu na cikin Gwamnan da ke goyon bayan kada a cire wannan tallafi. Da lamarin ya yi kamari Shugaban kasar America President Bush ya ce zai kawo ziyara Nigeria a July 11, 2003. Kafin Bush ya kawo ziyarar ne shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya daidaita da NLC akan ya fasa cire 50% na man fetur, amma maimakon haka su yarda a kara farashin man fetur ya koma N34. Wanda anan ne aka cin ma matsaya.
2. A January 1, 2012 ma, Goodluck Jonathan ya cire tallafin Mai gaba daya. Cire tallafin mai din ya sa farashi fetur ya tashi daga N65 zuwa N141. Wannan yunkurin shi ma bai samu karbuwa ba sakamakon mummunar zanga-zangar da Yan Nigeria su ka yi. Cikin wadanda su ka shiga zanga zangar har da tsoron shugaban kasa Buhari, El-rufai, Shugaban kasa na Yanzun Bola Ahmed Tunubu, da sauran jiga-jigan yan siyasa a fadin Nigeria. Zanga-zangar da aka sanya wa suna *Occupy Nigeria’, ta samu halartar shahararrun mutane kamar su Chimamanda
Adichie, Chinua Achebe, Wole Soyinka da sauransu. A wannan zanga zangar ma sai da jama’an tsaro su ka budewa masu zanga-zangar wuta, mutane 44 su ka raunata, yayin da mutane 11 suka mutu. Zanga-zangar ta dauki kwanaki 6 January 2012 har zuwa 16th January 2012 da aka cimma matsayar a sayar da mai a farashin N97.
3. Hatta Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yunkurin cire tallafin mai a 2016, amma yanayin yadda jama’a su ka nuna rashin amincewarsu da samun labarin yunkurin cire tallafin gaba daya ya sa dole Buhari ya hakura, maimakon haka sai Gwamnati ta sanar da karin farashin mai daga N86 zuwa N145. Ko a shekarar 2021 ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi yunkurin cire tallafin mai gaba daya amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba. Sai dai duk da haka sai da aka kara farashin mai din zuwa N164.85.
Mai karatu idan ka lura Gwamnatoci da yawa sun yi ta kokarin cire tallafin mai gaba daya amma hakar su ba ta cimma ruwa ba. Duk da haka dai za ka ga suna rage wani kashi na tallafin mai din.
TOH, WAI MAI YA SA SHUGABANIN KE SON CIRE TALLAFIN MAI DIN, KUMA MAI YA SA CIRE TALLAFIN MAI GABA DAYA KE GAGARA?
wannan shi ne abin da za mu cigaba da bayani a rubutu na gaba. Mai karatu ina biyo maka abin ne daki-daki domin ka fahimci yadda tallafin mai ya ke da badakalar da ke cikinsa. Idan kana bina a sannu a sannu za ka samu duk bayanin da ka ke bukatar sani game da cire tallafin mai.