SHIN YA HALLATA NA YIWA WANI ƊAWAFI ?
Tambaya;
Salam Malam. Menene hukuncin yin ɗawafi ga wani? Saboda mutane suna yawan cewa in naje Makka nayi musu ɗawafi.
Amsa:
Wa alaikum assalam. To, ƴar uwa babu wani dalili ingantacce wanda yake inganta yiwa wani ɗawafi, sannan kuma ba’a samu magabata na ƙwarai suna yi ba, gashi kuma ɗawafi ibada ce, ita kuma ibada ba’a yin ta sai da dalili daga Al’Qur-ani ko Sunnah. Amma dai ana iya yiwa wani addu’a lokacin da mutum yake yiwa kansa ɗawafi.
Akwai dalilai da yawa waɗanda suke nuna ingancin yiwa wani Umara ko Hajji, sai dai ba’a samu na ɗawafi a karan-kansa ba, ƙiyasin ɗawafi akan Hajji da Umara ba zai yiwu ba, saboda ɗawafi tsantsar ibadar jiki ce, Hajji da Umara kuma ibadu ne da suka haɗa jiki da dukiya. Duk ibadar da ta haɗa jiki da dukiya tana amsar wakilci, amma wacce ake yin ta da jiki kawai ba ta amsar wakilci, kamar Sallah.
Duba Fatawaa Nurun Aladdarb mai lamba (87).
Allah ne mafi sani
08/12/2014
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.