AMARYATA TANA MIN TSAKI, MENENE SHAWARA ?
Tambaya:
Assalamu alaikum Mallam Akwai wani daya kirani Yake cewa: yayi aure ne asali suna san juna da matar, amman iyayanta kaman basa san abun, so itama yarinyar tana mai wasu halaye, har yakai idan yana mata fada tana ramawa, ko tamai tsaki ma, Ana hakan ne sai ya wayi gari yaji gaba daya ya daina santa ko kadan, Mallam menene mafita?
Amsa:
Wa alaikum assalam,
To dan’uwa zai yi kyau şu bi matakan da Allah ya fada a suratunnisa’i na matar da ta butsare, ta yadda zai yi Mata wa’azi, in ta ki ya kaurace mata, in hakan bai yi amfani ba sai a kira zaman sulhu, a samu wakilai daga bangaren matar, wasu daga bangaren mijin, in har sun yi nufin gyara Allah zai datar da su.
In har wadannan matakan ba su yı amfani ba, suna iya rabuwa, Allah kuma mai iko ne ya azurta kowa daga falalarsa, ya bata wanda za su yi daidai, shi ma ya samu wadda za ta iya zama da shi, kamar yadda aya ta: 130 a suratun Nisa’i ta tabbatar da hakan.
Hakuri shi ne ginshikin zaman aure, saidai idan mushkiloli suka yi yawa, aka kasa yi musu hanci, to babu zaman doya-da- manja a musulunci, Allah ya shar’anta saki ne domin tunkude cuta daga daya daga cikin ma’aurata, ko kuma su duka.
Allah ne mafi sani
Amsawa✍????
Dr. Jamilu Zarewa
2\3\2016