Karanta addu’ar shiga banɗaki, baayi, bayan gida ko kuma toilet
Manzon Allah (S.A.W) ya koyar da addu’o’i iri biyu, duk wanda kayi dai dai ne, na farko in zaka shiga ko kace “Bismillah”, Sahihul Bukhariy, Hadisi na 142.
Ko kuma kace “Allahumma inni a’uzu bika Minal khubsi wal khabaa’is”, Kafin ka shiga.
Karanta Sunan Ibnu Maajah, Hadisi na 297.
.
Manzon Allah yace “kariya, tsarin dake hana Shedanun al-Janu suga al-aurar ‘dan Adam a lokacin da ya shiga Baayi, shine yace Bismillah yayin da zai shiga”.
Abubuwan lura guda biyu:
Idan ka karanta ‘daya daga cikin addu’o’in nan yayin da zaka shiga, manzon Allah ya tabbatar cewa Aljanu ba zasu iya ganin ka ba a lokacin da kake bandakin.
Yadda baka iya ganin su da idon ka toh haka suma ba zasu iya ganin ka ba, idan kayi addu’ar yayin shiga bayan gida.
.
2. Abu na biyu, Malamai suka ce:
Rashi yin addu’ar yana daga cikin dalilan da suke hana haihuwa, yana illa ga maza da mata rashin yin addu’ar shiga bandaki yayin shigar.
Idan mutum ya shiga bandaki bai yi addu’ar ba toh baya da wata kariya daga shedanun Aljanu, yayin da yake fitsari zasu rike gaban sa, su kulle, su daure, dan haka zai iya yin fitsari amma ba zai iya samar da ‘ya’ya ba.
Zaka ga wasu anyi-anyi amma bata haihuwa ko baya haihuwa, duk magani anyi amma abu ya gagara.
.
Ba komai bane kulli ne Aljanu suka yi ma al-aurar sa, idan macece kuma sai su ‘daure kan mahaifar ta, dan haka ba zata haihu ba, ko ta samu ciki sai ya zube.
Babban dalili shine Aljanu ne suka samu dama akan mutum yayin da shiga wurin zaman su, shine bandaki (Toilet).
Zasu gan shi da idon su, zasu ga al-aurar sa, kuma zasu iya masa illa a lokacin.
Bayanai ne masu fadi, masu yawan gaske, kuma masu muhimmanci.
.
Karanta littafin “Wiqayatul Insaan”.
Da littafin “As-sarimul battar”, dukkan su na Sheikh Waheed Abdus-salaam Baaliy.
Da littafin “Ad-daa’u wad dawa’a”, na Ibnul Qaiyyim al-Jauziy.
Tare da littafin “Al-Wabilus sayyib” shima na Ibnul Qaiyyim.
Da kuma littafin “Al-azkaar”, na Imamun Nawawiy.
Allah yasa mu dace, mu kuma kiyaye.
✍️
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.