Tambayoyi a MusulunciTech

AMFANI DA NA’URAR “P.O.S” LOKACIN CIRAR KUDI



Tambaya
Assalamu alaikum, Malam menene hukuncin amfani da na’urar “P. O. S” yayin cirar kudi, Maimakon mutum ya je banki, sai ya je ya bawa wani lambarsa ta banki, sai ya yi amfani da na’ura ya juya kudin zuwa na shi banki, sai ya ba shi su a hannu tare da amsar lada?

Amsa
Wa’alaikumus Salam, To dan’uwa amfani da P.O.S. zai iya shiga cikin kiyasu-Ashshabah (قياس الشبه) a ilimin Usulul fiqh, saboda idan aka kalli P.O.S ta wani wajen yayi kama da haramun domin za ka bada dubu goma a baka naira (9,800), saboda a wurare da yawa duk dubu daya suna amsar ladan naira 20 ne, to kaga ta nan wurin zai iya zama haram kasancewar an samu fifiko, a tsakanin kudi da kudi, samun fifiko kuma tsakanin kudi da kudi haramun ne.

Akwai kuma bangaren da zai iya zama halal idan aka kalli cewa mai cirar kudin an rage masa wani abu na lokacinsa tun da idan banki mutum zai je ya ciri kudin zai hau mota zai bata lokaci, sannan kuma banki duk withdrawing din da za ka yi in dai conventional bank ne akwai abinda za su cira daga cikin account dinka, ka ga ta nan bangaren zai iya zama halal kasancewar aiki mai P.O.S ya yi aka biya shi.

Akwai fatawar malamai a Saudiya wadanda suke ganin cewa idan mutum ya ajjiye kudi a banki kuma kudin nasa ba su da yawa, ya l halatta bankin ya dauki wani abu na ladan aikinsa, saboda wahalar da ya yi na kula da kudin, a bisa wannan fatawa P.O.S zai iya zama ya halatta kasancewar mutum aiki ya maka ya kuma rage maka lokaci sannan kuma ya wakilceka a charges din da banki za suyi maka idan za ka ciri kudi daga account dinka.

Duk mutumin da bai shiga bukata ba kar ya yi amfani da P.O.S a irin sigar da ake amfani da ita a Nigeria, saboda ladan da ake amsa ya fi kudin da banki yake caja, sannan nisantar shubuha ginshike ne a sharia, amma wanda ya shiga lalura ya halatta ya yi amfani da shi gwargwadon lalurarsa saboda abin da ya gabata.

Allah ne mafi sani

13/04/2019

Dr. Jamilu Zarewa.

See also  HANYAR DA ZAKA BI KA GANE LOGO ƊIN DA KA ƙIRƙIRA IDAN AN TAƁA SAMAR DA IRIN SHI

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button