RamadanTambayoyi a Musulunci

JININ BARI BA YA HANA AZUMI

Tambaya
Assalamu alaikum, malam ina da tambaya, Don Allah idan mace ta yi barin ciki na wata biyu wannan jinin ya zama na ciwo ko za ta daina azumi sallah ?

Amsa
Wa alaikum assalam To dan’uwa wannan jini ba zai hana sallah da azumi ba, saboda ba jinin haihuwa ba ne, malamai suna cewa : duk cikin da ya zube kafin a busawa yaro rai, to ba zai hana sallah da azumi ba, ana busawa yaro rai idan ya kai watanni hudu a ciki, kamar yadda hadisin Ibnu Mas’ud, wanda Bukhari da Muslim suka rawaito ya nuna Hakan,.
Saboda haka duk cikin da ya zube kafin haka, to jininsa, ba zai hana sallah ba, ba zai hana azumi ba, amma mutukar an busawa yaro rai ko kuma halittarsa ta fara bayyana, to za’a bar sallah da azumi.

Allah ne mafi sani.

DR. JAMILU YUSUF ZAREWA

30/03/2023

See also  MALAM ZAN IYA ADASHI DA WANDA BA MISULMI BA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button