Tambayoyi a Musulunci

INA FAMA DA CIWON ƘODA, ZAN IYA CIYARWA A MAIMAKON AZUMI ?

Tambaya:
Assalamu Alaikum. Malam ina da tambaya. Mace ce ba ta da lafiya, ciwon ƙoda ya fara tsananta gare ta, sai satinnan Likitoci suka ba ta shawara duk bayan minti talatin ta ci wani abu daga abinci amma kar ta ƙoshi, to Malam yaya za a ɓullowa maganar azumin da ta sha? ciyarwa za a ci gaba da yi ko jira za a yi sai ta warke ta rama?

Amsa:
Wa alaikum assalam. In har tana tunanin samun sauƙi nan gaba, ba za ta ciyar ba, za ta bari ta rama bayan ta samu dama, saboda aya ta (184) a suratul Baƙara ta nuna cewa: wajibin mara lafiya shine rama azumin da bai yi ba na Ramadhana bayan ya samu dama a wasu kwanakin.
Matuƙar Likitoci sun tabbatar ba za ta samu sauƙin da za ta rama Azumi daga baya ba, ya halatta ta ciyar a maimakon azumin kowacce rana.
Allah ne mafi sani.
26/6/2016

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

See also  NA YI JIMA'I A RAMADHANA, AMMA BA ZAN IYA KAFFARA BA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button