TechWhatsApp

Yadda ake tura Hoto, Video, Waƙa ko kuma wani file a matsayin document ta whatsapp


Idan baka iya ba ka daure ka iya, idan kuma ka iya dan Allah ka koya ma na kusa dakai domin muhimmancin abun.

‘Dan ƙaramin abunda ka raina mafi yawan wasu mutanen basu iya shiba, kuma badan rashi ilimi bane ko wayewa, kawai dai basu san ya akeyi bane.

Amfanin tura video ko pictures a matsayin document ta whatsapp shine basa rage resolution, wato ma’ana basa rage quality kafin su isa wajen wanda ka tura mawa.

Yanayin cigaban da aka samu a wannan zamanin ta fuskar ilimin kimiya da fasaha yasa ana ƙulla alaƙa ta nesa da mabanbantan mutane ta hu’d’dar kasuwanci, aiki, karatu da sauran mu’amulolin yau da kullum.

Sau da yawa wani zaiso yace ko kuma hakan ta kama dole zaka tura mashi wani hoto ko video wanda dakai dashi ‘din dukanku bakwa buƙatar abun ya rage quality duba da zata iya kasancewa aiki za’a ayi da abun ta wani fannin, idan irin hakan ta kama kaga cikin sau’ki zaka tura mashi idan har kasan ta yadda zaka tura mashi.

Tura hoto ko video a matsayin document yafi bada gudunmuwa ga masu sana’ar ‘daukar hoto ko kuma masu aikin graphic design.

Mafi yawan lokuta mai daukar hoto ko mai aikin graphic design zasu gama aiki su gyarashi sosai amma da zaran sun tura ma wanda sukayi ma aikin sai yace aikin beyi mashi ba, ko yace hoton da aka daukeshi ‘din ba’a gyarashi da kyauba, alhalin kuma an gyara, kunga rage quality ‘dinda aikin yayi akan iska yayin da ake turashi shine yasa akace aikin baiyi yadda akeso ba.

Duk hoto ko video wanda ka tura a matsayin document ka tabbata bazai ta6a rage quality ba kafin ya isa zuwa inda ka turashi, yadda kasan ka turashi ta email haka zai kasance.

Idan kuka duba a hoton da yake sama nayi misalai guda uku 3 wa’danda zasu jagorance ka wajen tura hoto, video, waƙa ko wani file a matsayin document.

Matakin farko zaka shiga cikin gurbin inda kuke zantawa da wanda zaka tura ma saƙon, zaka danna ma6allin za6ar tura saƙo, zai baka damar za6ar irin kalan saƙon da kakeso ka tura.

Mataki na biyu kuma zaka danna madannin za6in “Document”

Mataki na uku shine idan ya bu’de sai ka danna wasu layuka guda uku wanda suke inkiya akan baka damar nemo shi abunda zaka tura ‘din a matsayin document.

Daga nan sai ka za6a inda kake son ka shiga dan ganin abunda zaka tura cikin sauƙi.

A lura da wajen da aka saka…
-Recent ana nufin gurbin sabbin file da suka shigo wayarka bada da’dewa ba.

-Download kuma gurbi ne na abubuwan da kayi download da kanka wanda ba wanine ya tura maka ba, kaine ka samosu daga saman yanar gizo kuma ka saukesu a cikin wayarka.

-Drive nan kuma yana bayanine akan abubuwan daka adana acikin gidan ajiyarka na yanar gizo wanda a saman iska yake.

Masha Allah.

Karku kalli wannan a matsayin ‘dan ƙaramin abu, karku yi mamaki idan nace maku wanda basu san yadda akeyinshi ba sunfi wanda suka sani yawa.

Babu tantama hakane, kuma laifin rashin iyawarsu yafi yawa akaina dakai mu da muka iya muka kasa koya masu yadda akeyi.

Ku sani wasu suna son tambayar wani abun amma suna jin kunyar tambaya dan kada ace basu iya ba, to tunda mun fahimci hakan mai zai hana mu dunga sanar dasu tun kafin su tambayemu?

Allah yasa mu dace, Amin.

✍???? Abu Ibrahim

See also  YADDA ZAKU IYA DAWOWA DA DUK WANI MESSAGE NA WAYARKU DAYA GOGE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button