KAMANCECENIYAR CRYPTOCURRENCY DA ZINARE.
Cryptocurrency kamar karafuna masu daraja ne (Precious metals) da ake haƙowa a karkashin kasa misali, zinare, azurfa da sauransu. Karafuna masu daraja ana haƙo su ne a karkashin kasa, hakan na nufin babu wani kamfani ko mutum dake iya amfani da wani abu wajen kera zinare ko azurfa da sauransu. Suma cryptocurrencies da zarar an ƙirƙire su ƙirƙirar farko suna zauna ne a database (rumbun ajiya na computer) an tsara su ta hanyar da mutane za su yi wani yunkuri mai kama da haƙo wajen haƙo su daga cikin database din. Ana hako zinari ne ta hanyar da ake kira “Gold mining” yayin da ana hako cryptocurrencies ne ta hanyar da ake kira da “cryptocurrency mining”
Gold mining: Hanyace ta da amfani karfi, lokaci da kayan tono wajen domin hako zinare daga karkashin kasa. Galibi mutane sukan yi aikin tukuru da ake buƙatar juriya da kokari domin haƙo zinare daga karkashin kasa. Kasancewar zinare a matsayin abu mai daraja da yake da tsada wajen saye, da kasancewarsa ba’a iya kera shi dole sai dai a hako shi daga karkashin kasa, wannan ne ke sanyawa mutane ke dagewa wajen ganin sun hako zinaren. Wahalar da ake yi wajen haƙo shi yana daga cikin abinda yasa yake da daraja saboda ba kowa zai iya haƙoshi ba.
Cryptocurrency mining: Hanyace da mutane ke yin gasa wajen magance matsalar lissafi domin samun ladar cryptocurrency. Cryptocurrency ba kamar zinare bane da ake hako shi a karkashin kasa, domin samun zinare dole sai dai ka haƙo ko kuma ka saya a wajen wani. Haka domin samun cryptocurrency dole sai dai ka aiwatar da wasu ayyuka (zamu yi bayanin su a gaba) ko kuma ka saya a wajen wani. Ayyukan da zaka aiwatar wanda suke bukatar amfani da software ko hardware wajen samun cryptocurrency ana kamanta wannan aikin da hakowa irin wanda akewa zinare.
Ta wannan hanya da ake kira “Mining” za’a iya cewa zinare da cryptocurrenies suna da kamanceceniya.
Dukkaninsu suna da iyaka
Gaba daya nau’ikan kudade Cryptocurrency suna da adadin da aka iyakance na samar da su wanda ba zasu taba wuce guda adadin nan ba. Misali Bitcoin guda billion 21 ne za’a iya haƙowa a database, wannan adadin ne zai yi yawo a hannun mutane. Da zarar an gama haƙo adadin to hanyar samun Bitcoin zai kasance ta hanyar sayensa a wajen wani kadai, wanda hakan ne yasa yan kasuwa ke rububin sayensa, kuma haka ne yasa kowanne cryptocurrency darajarsa kullum kara karuwa take sakamakon kullum adadinsa karuwa yake.
Koda yake zinari bazai iya karewa da sauri kamar Bitcoin ba, amma bincike ya nuna cewa samun zinare a karkashin kasa na iya raguwa nan da shekara ta 2050. Wannan zai faru ne saboda mutane zasu gama fitar da dukkan “zinare mai saukin samu” daga wannan lokacin sai dai an sha wahalar zurfafa tono kafin a iya samun zinaren. Dalilin hakane masana suka ce zinare shima wata kadara ce mai iyaka.
Dukkaninsu ana iya saye aje a matsayin kadara.
Saboda dukkanin su suna da iyakantattun adadi da kyakkyawan tsaro wajen ajiya hakan yasa da yawa yan kasuwa suke sayan su suna ajewa da hasashen zasu kara farashi zuwa gaba su sayar. Idan muka bincika tarihi zamu ga farashin zinare shekara goma (10) bai kai yanzu ba, domin zinare yafi saukin samu a shekarar goma (10) da ta wuce fiye da yanzu, kullum hakowa ake kullum kara wahalar samu yake.
Haka cryptocurrency kamar Bitcoin farashinsa N7,220 kowanne ɗaya a 2009 yayin da yanzu N20,284,334 a wannan shekarar ta 2021. Zinare a matsayin kadara za’a iya kamanta da Bitcoin.
Amma kudaden takardu kamar Naira ba zaka iya saye ka aje da tunanin zasu kara kudi ka sayar zuwa gaba ba, maimakon su kara daraja zai iya yuyuwa darajar su ta ragu kasancewar su cigaba ake da bugo su batare da iyaka ba. Sannan zai iya yuyuwa daga baya gwamnati ta shafe amfani da su kamar yadda gwamnati ta hana amfani da wasu kudaden a Nigeria sakamako chanja sabbi.
Tabbass, duk abinda ke da tsaro wajen ajiya, ba’a iya buga na bogensa, yake da daraja sannan yake da adadi ba shakka dole abin ya kasance kadara mai kima da za’a iya saye a aje.