Tech

Yadda zaku bude lambarku ta telegram da aka rufe

Mafi yawan complain da muka dunga samu a wannan shekarar na wasu daga cikin dalibanmu da suke karatu a azuzuwanmu dake telegram shine: an rufe masu lambarsu ta telegram ma’ana anyi “banned” nata.

Abu mafi muhimmanci da ya kamata mu fahimta shine: duk wani kamfani da yake da mallakin wata manhaja da ake amfani da ita to shima kamar shago ne na kasuwanci, bazai ta6a yarda ya rasa kwastoma ba da gan-gan sai dai idan har kwastoma din zai jaza mashi wata fitina tsakaninshi da wasu kwatomomin.

Dan haka da telegram da whatsapp da sauran wasu manhajojin da muke amfani dasu idan har kaga sun dakatar da lambarka to akwai dalilin yin hakan, ka taka wata doka tasu ne ko kuma anyi wani laifi ne daya shafe ka kuma akayi report na laifin.

Duk lokacin da irin hakan ta faru da kai ko wani na kusa da kai, babu wata mafita mai sauƙi data wuce a sanar da su kamfanin da suke da manhajar, dan daga garesu ne zasu iya gyara ma mutun matsalar a cikin lokaci.

Yin report zuwa ga wani kamfani ba abu bane mai wuya, amma dai ga wanda baisan yadda ake yi ba yakan d’an bashi wuya kad’an.

Ga matakan da zaka bi nan dan bude lambarka ta telegram da aka rufe:

1- Da farko zaka shiga kai tsaye cikin manhajar telegram dinka, inda zasu baka damar saka lambar wayarka kamar zaka bude sabon account, daga nan manhajar telegram din zata sanar da kai cewa lambarka anyi banned nata, tare da wasu rubutu masu alamar za6i guda biyu “Edit da kuma Help” sai ka danna help d’in zai dauke ka kai tsaye zuwa cikin email dinka wanda ke saman wayarka domin samun damar tura masu saƙon ƙorafi.

See also  YADDA AKE UNBANNED WHATSAPP NUMBER

2- Bayan ka shiga cikin email din za kaga email address nasu ya bayyana kamar haka “recover@telegram.org” daga ƙasan inda email address naka ya bayyana, kuma za kaga an rubuta “Banned phone number: lambar wayarka”, sai wani rubutu mai dvan yawa kamar haka:
I’m trying to use my mobile phone number: (lamabar wayarka) sai But telegram says it’s banned. Please help. Sai kuma wasu bayanai na game da ita kanta wayarka d’in da version na telegram da kake amfani dashi da sauran wasu bayanai kad’an.

Abunda za kayi anan shine: sai kaje daidai inda rubutun farko ya ƙare wajen help kenan sai ka dawo ƙasa kad’an ka rubuta : I need this account it’s on my most used number, sai ka koma daga ƙasa kasa thank you.

Rubutun ya kasance kamar haka:
I’m trying to use my mobile phone number: lamabar wayarka sai But telegram says it’s banned. Please help.

I need this account it’s on my most used number.

Kaga daga ƙasa sai sauran bayanannan na OS, Device da kuma Version kenan,

sai kuma “Thank you” da zaka rubuta daga kasan

Daga nan sai ka danna send, zai tafi kai tsaye wajensu.

3- Mataki na gaba kuma zaka tafi ne zuwa cikin browser dinka kamar irin ko google chrome sai ka saka: “telegram.org/support” sai ka danna go, idan ya bude zai nuna maka wasu gurabe da zaka cike da rubutu har guda uku.

Na farko da aka rubuta: “please describe your problem” sai ka shiga ka cikeshi da rubutu kamar haka: “My number (sai kasa lambarka) has been banned and I’m not able to figure out the reason for suspension, please help me to recover my account.

See also  YADDA ZAKU YI DOWNLOAD NA VIDEOS DIN PINTEREST DA WAYARKU

Thank you.

Na biyu inda aka rubuta: “Your email” sai kasa email dinka.

Na uku inda aka rubuta: “Your phone number” sai kasa lambarka.

Daga nan sai ka danna submit, zasu nuna maka wani koren rubutu daga sama sunce: “Thank you for your report! We will try to reply as soon as possible”.

Shikenan ka kammala komai, insha Allah bayan mintuna kad’an da kaje ka sake saka lambarka kamar zaka bude sabon accoun za kaga sun barka ka wuce ba tare da sun ƙara ce maka anyi banned na lambarka ba.

Allah ya taimaka.

Abu Ibrahim

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button