RamadanTambayoyi a Musulunci

TAFIYA TA KAMA NI A TSAKIYAR YINI, KO ZAN IYA KARYA AZUMINA ?



Tambaya:
Assalamu Alaikum. Mutum ne zai je Umara cikin Azumi, sai ya zama jirginsu zai tashi ƙarfe biyu na ranar, shin zai kame baki ne daga safe zuwa lokacin tashin ko kuwa ba zai yi Azumi ba kwata-kwata a ranar?

Amsa:
Wa alaikum assalam. Zancen mafi yawan Malaman Hanafiyya da Malikiyya da Shafi’iyya shine: Idan mutum yayi tafiya a tsakiyar yini, to ba zai ci abinci ba, saidai idan ya shiga wahalar da ba zai iya jurewa ba. Amma a wajan Malaman Hanabila ya halatta, saboda Allah ya halattawa matafiyi cin abinci a suratul Baƙara kuma bai bambanta tsakanin wanda yayi tafiya a farkon yini ba da wanda yayi a tsakiya.
Don neman ƙarin bayani duba: Al’insaf, 3/205
_Allah ne mafi sani._
21/06/2015

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

See also  INA RUBUTAWA DALIBAI WAEC, MENENE MATSAYINA ?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button