Tambayoyi a Musulunci

HUKUNCIN BOYE KAYA HAR SAI SUN YI TSADA



Tambaya :
Assalamu alaikum.malam wata tambaya nake da ita Dr. Wai shin meye gasiyar hukuncin wanda ya sayi kaya a lokacin da suke araha ya boye da niyyar in sunyi tsada ya fito da su ya sayar dan ya sami riba mai yawa? Allah shi dada budi amin

Amsa :
Walaikum assalam To dan’uwa ya zo a hadisi cewa : “Ba wanda yake boye kaya sai mai zunubi” Tirmizi ya rawaito shi a : 3\567, kuma ya kyautata shi, saidai malamai sun yi sabani akan irin kayan da ya haramta a boye da wadanda ba su haramta ba :
1. Akwai wadanda suka tafi cewa : duk wani abu da mutane suke bukatarsa to bai halatta mutum ya siya ya ajjiye ba, da nufin sai yayi tsada ya fito da shi, don haka har tufafi da magunguna bai halatta a boye su ba, saidai idan ya siya ne da nufin ya yi amfani da su nan gaba. Ko kuma iyalansa, Wannan shi ne maganar Abu-Yusuf babban almajirin Abu-hanifa, kamar yadda yazo a littafin : Daurul-kiyam wal’aklak fil-islam shafi na : 295. Sannan ita ce maganar Malik a Mudawwanah kamar yadda ya zo a : 4\291.
2. Akwai malaman da suka tafi cewa ya halatta a boye abin da yake ba abinci ba ne da mutane za su ci su rayu, kamar barkono, zabibi, mai, da sauransu, saboda yawanci mutane suna cutuwa ne idan aka boye abinci. An rawaito wannan daga Abdullahi dan Mubarak da Sa’id dan Musayyib kamar yadda Tirmizi ya ambata a Sunan dinsa 3\567 sannan ita ce maganar Shafi’iyya da Hanbaliyya , kamar yadda ya zo a
Raudatu Addalibiina 3\411 da kuma Almugni 4\154

Wasu malaman suna rinjayar da maganar farko, amma idan ba siyan abin ya yi ba, ya mallake shi ne ta wata hanya, ko kuma ya noma sai ya boye har ya yi tsada sannan ya siyar, to wannan bai haramta ba, ko da kuwa abinci ne, har wasu malaman ma sun hakaito ijma’in malamai akan halaccin haka, kamar yadda ya zo a Jami’ussagir shafi na : 481

Allah ne mafi sani
DR. JAMILU YUSUF ZAREWA
15/8/2014

See also  ANNABI MUHAMMAD (SAW) BA YA KASHE WANDA YA ZAGE SHI !

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button