Addu'o'i
Karanta Addu’ar Wanda Ya yi Atishawa
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce Idan mutum yayi Atishawa sai yace:
الْحَمْـدُ للهِ.
Alhamdu lillah.
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah.
Dan’ uwansa kuma ko wanda yake zaune tare da shi ya ce masa;
يَرْحَمُكَ اللهُ.
Yarhamukal-lah.
Allah Ya ji kanka.
Idan ya gaya masa haka, shi kuma ya ce masa:
يَهْدِيكُمُ اللهُ وَيُصْلِحُ بَالَكُمْ.
Yahdeekumul-lahu wayuslihu balakum.
Allah ya shirye ku, Ya kyautata halinku.