RamadanTambayoyi a Musulunci
MACE ZA TA IYA YIN I’ITIKAFI ?
Tambaya:
Assalamu Alaikum Malam. Menene hukuncin ittikafin mata a Musulunci?
Amsa:
Wa alaikum assalam. Ya halatta mace tayi i’itikafi, saboda matan Annabi (S.A.W.) sun yi I’itikafi kamar yadda ya zo a Sahihul Bukhari.
Yana daga cikin ƙa’idoji a Usulul-Fiqhi duk hukuncin da ya zo a Shari’a yana haɗe mata da maza, sai idan an samu dalilin da ya keɓance maza kawai.
I’itikafi ibada ce tabbatacciya a Musulunci wacce Annabi (S.A.W.) ya aikata ta saboda neman kusanci da Allah a watan Ramadhana, babu bambanci tsakanin mace da namiji wajan koyi da Annabi (S.A.W.) a wannan ibadar, saidai kar matar aure ta fita sai ta nemi iznin mijinta.
Allah ne mafi sani.
28-06-2016
Dr. Jamilu Yusuf Zarewa