Karanta Addu’ar Sanya Sababbin Tufafi
Akwai bambanci tsakanin addu’an da ake yi yayi sanya sabon tufafi da kuma tufafin da muke sakawa kullum, shi wannan addu’ar a na yin shi ne yayi da ka sayo sabon tufafi wanda baka taɓa saka shi a jikin ba. Sai ka karanta wannan addu’ar dake ƙasa:
“اَللَّهُمَّ لَكَ الْحَمْدُ أَنْتَ كَسَوتَنِيهِ، أَسْأَلُكَ مِنْ
خَيْرِهِ وَخَيْرَ ماَ صُنِعَ لَهُ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهِ وَشَرَّ مَا صُنِعَ لَهُ.
Allahumma lakal-hamdu anta kasawtaneeh, as-aluka min khayrihi wakhayri ma suni’a lah, wa-a’u’zu bika min sharrihi washarri ma suni’a lahu.
Ya Allah! Dukkan yabo ya tabbata gare Ka, Kai ne Ka tufatar da ni shi (wannan tufar). Ina rokonKa alherinsa da alherin abin da aka yi shi dominsa, kuma ina neman tsarinKa daga sharrinsa da sharrin abin da aka yi shi dominsa.
Domin karanta addu’an da ake yi yayin sanya tufafin mu na yau da kullum sai a shiga Link din dake ƙasa